Wani matashi mai suna Dada ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta wanda ya kai shi da komawa hawa kujerar guragu, BBC News Nigeria ta ruwaito.
Kamar yadda ya bayyana a mawuyacin yanayi inda aka nuna hotunansa lokacin yana da lafiya da kibarsa, daga bisani kuma ya kankance kuma ya yi matukar ramewa.
KU KARANTA: Nawa zai cira haka: Bidiyon matashi yana sharar bacci a gaban ATM ya ɗauki hankula
Bisa yadda aka wallafa, matashin ya ce: “Sunana Dada. Na samu ciwo a kashin gadon baya da kafa kuma na koma amfani da keken guragu.
Ba a haka aka haife ni ba. Dakyar na tsira daga mutuwa. A shekarar 2021 na tsinci kaina a asibiti inda na yi zaman ICU wanda rayuwa ta sauya gabadaya.
“Na cigaba da zama a kujerar guragu inda ba na iya zama saboda duk kafafuna suka shanye, fitsari ma sai ta roba saboda na koma fitsari a famfas. Iyayena sun juya min baya.
“Da matata nake ta rayuwa wacce ta cigaba da min duk wani kokari saboda a kullum ina amfani da famfas biyu, kuma duk fakiti N1,000 ne.
“Ina whan wahala dare da rana kuma yin amfani da tsohon famfas na kara tabarbara rayuwata. Ina neman taimakon N400,000 za a min aiki. Ni da iyalina ba mu da hali, idan kana da N1000, N2000, 3000 ko sama da haka.
“Ga asusun bankina 3193258933, first bank plc, sunana Obasio P. Dada.”
An kwashi ‘yan kallo yayin da matashi ya ciccibi katifa, murhu da tukunya zuwa banki don jiran kuɗi
An kwashi ‘yan kallo yayin da wani dan Najeriya ya lallaba zuwa banki da cikakken shirinsa din jiran amsar kudi, Legit.ng ta ruwaito.
Matashi ya bayyana a bankin da katifa, murhun gas da tukunya don yin aikace-aikacensa na gida kafin ya amshi kudinsa daga banki.
Nan da nan kwastomomi suka sha mamaki inda suka nuna goyon baya a gare shi inda suka ba shi masauki tare da jera masa kayan yadda ya dace.
Mutane da dama sun nuna rashin jindadinsa dangane da yadda bankuna suke tafiyar da lamurransu a kan kudade.