Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya kashi 96.75 na sakamakon zanen gwamnan Ogun da aka yi ranar Asabar a shafinta na kallon sakamakon zabe.
Da misalin karfe 9:30 na safiyar Lahadi, an saka sakamakon zaben runfuna 4,878 daga cikin rumfunan zabe 5,042 a Ogun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Kano: Shekarau Ya Sha Kayi A Akwatinsa
Wakilin Majiyar Dimokuradiyya ya ruwaito cewa, ba a gudanar da zaben a wasu rumfunan zabe ba, sakamakon hare-hare da sace akwatin zabe.
INEC ta ce daga yanzu za a fara tattara sakamakon kowace karamar hukuma.
DAILY POST ta rahoto cewa zaben ya fi zafi ne tsakanin Gwamna Dapo Abiodun na jam’iyyar APC da Ladi Adebutu na jam’iyyar PDP a matsayin manyan ‘yan takara biyu.
A waji labarin kuma, DA DUMI-DUMI: PDP ta lallasa APC tare da lashe kujerar majalisa dokoki ta farko a jihar Kogi
An bayyana dan takarar jam’iyyar PDP na karamar hukumar Ogori Magongo a jihar Kogi, Bode Ogumola, a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar dokokin da aka gudanar ranar Asabar a jihar