Tsohon gwamna Kano Malam Ibrahim Shekarau ya fadi zabe a akwatinsa da dake giginyu Firamare a mazabar giginyu dake karamar hukumar Nassarawa.
Daga cikin kuri’u 218 da aka kada a akwatunsa, jamiyyar sa ta PDP ta samu nasarar lashe kuri’u 3, sai jamiyyar APC wadda ta samu kuri’u 89, yayin da jamiyyar NNPP ta samu kuri’u 119.
KU KARANTA: Kano: Abba Kabir Yusuf Ya Lashe Zaben Karamar Hukumar ta Farko
Sanata Ibrahim Shekarau shine sanatan Kano ta tsakiya yanzu haka mai baring ado, bayan da aka zabi Sanata Hanga a matsayin wanda zai gaje shi tsawon shekaru hudu nan gaba.
Malam Ibrahim Shekarau ya taba zama ministan Ilimi na tarayya zamanin mulkin tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan.
A wani labarin kuma: Kwankwaso Yayi Nasarar Lashe Akwatinsa
Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya nasarar lashe akwatin sa, a zaben gwamna dana yan majalisu da aka gudanar a jiya Asabar.
Sanata Kwankwaso wanda kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya ne ya samu kuri’u 4349 a zaben na gwamna, yayin da jamiyyar APC ta samu kuri’u 2468 a mazabar Kwankwaso dake karamar hukumar Madobi.