Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi, Alhaji Adamu Manu Soro, ya musanta cewa shi ne a cikin wani faifan bidiyo da aka yi zargin cewa yana sayen kuri’u ga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Bidiyon, wanda aka wallafa a shafin yanar gizon yanar na Twitter, ya fara yaduwa ne kafin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da aka yi ranar Asabar a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Kano: Shekarau Ya Sha Kayi A Akwatinsa
Da yake karyata faifan bidiyon da aka yi da shi a wata hira da manema labarai a Bauchi, kwamishinan ya bayyana cewa ba shi ne mutumin da ke cikin faifan bidiyon ba, inda ya kara da cewa da irin kwazon da gwamna Bala Mohammed ya yi tun hawansa mulki zai zama butulci kowa ya yi zargin cewa an siya kuri’a ga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.
“Wannan faifan bidiyo na Twitter da ke yawo a duniya, duk wanda ya san jihar Bauchi, ya san cewa Gwamna Bala Mohammed ya taka rawar gani a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata wajen gudanar da manyan ayyuka, don haka butulci ne a ce wani ya yi zargin siyan kuri’u a zabe mai zuwa domin PDP mai mulki a jihar.
“Ba ni ne wanda ke cikin faifan bidiyo da aka yada ba a duniya ba. Don haka duk wani ko wata kafar sadarwa ta wallafa wani labari daga faifan bidiyon na yin hakan ne don bata sunana da mutuncina a idon jama’a, kuma da yardar Allah zan dauki matakin shari’a a kan hakan,” in ji Manu Soro.
A wani labarin kuma, INEC ta wallafa Kaso 96 cikin 100 na sakamakon zaben gwamnan Ogun
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya kashi 96.75 na sakamakon zanen gwamnan Ogun da aka yi ranar Asabar a shafinta na kallon sakamakon zabe.
Da misalin karfe 9:30 na safiyar Lahadi, an saka sakamakon zaben runfuna 4,878 daga cikin rumfunan zabe 5,042 a Ogun.