DA DUMI-DUMI: PDP ta lallasa APC tare da lashe kujerar majalisa dokoki ta farko a jihar Kogi
An bayyana dan takarar jam’iyyar PDP na karamar hukumar Ogori Magongo a jihar Kogi, Bode Ogumola, a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar dokokin da aka gudanar ranar Asabar a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kano: Abba Kabir Yusuf Ya Lashe Zaben Karamar Hukumar ta Farko
Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta a kan zaben, Mista Ekundayo Mejebi, ya bayyana sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Magongo da sanyin safiyar Lahadi.
Ya ce dan takarar PDP ya samu kuri’u 2,910 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Manjo Akerejoka na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya samu kuri’u 2,162.