…Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta haramta duk wata zanga-zanga da ake shirin gudanarwa domin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa tana mai sanar da jama’a cewa an haramta duk wata zanga-zanga a fadin jihar.
Don haka ta ce an haramta duk wata zanga-zangar da aka shirya gabatarwa a ƙarƙashin kowane irin tsari.
Kakakin rundunar DSP Ramhan Nansel a madadin kwamishinan ya sandan jihar Nasarwa ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da jaridar DIMOKURADIYYA ta samu a ranar Lahadi.
KU KARANTA KUMA Yan Sanda Sun Ceto Mutane 30 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Nasarawa
Rundunar ‘yan sandan ta dauki wannan matakin ne domin hana tabarbarewar doka da oda da kuma dorewar zaman lafiya da ake samu a jihar a halin yanzu.
Don kuwa rahoton masu hankali kan tsaro ba zai iya ci gaba da kula gudanar da duk wata zanga-zanga a jihar ba.
Haka zalika an shawarci iyaye da masu kula da ‘ya’yan su da su tabbatar ‘ya’yansu da unguwanni ba su karya wannan umarni ba domin duk wanda aka kama za kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.
A Wani Labarin Kuma Zaben Gwamnonin Kogi, Bayelsa, Imo: APC Ta Samu Sama Da N1.3bn Daga Siyan Fom
Jam’iyyar APC mai mulki ta samu sama da Naira biliyan 1.3 daga sayar da fom din nuna sha’awar tsayawa takara ga ‘yan takarar gwamna a jihohin Kogi, Bayelsa da Imo da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba.
Jam’iyyar APC ta yi cinikin fom din a kan Naira miliyan 50 sannan ta sayar da su a shedikwatarta ta kasa da ke Abuja tsakanin ranakun 15 zuwa 22 ga watan Fabrairu, kamar yadda jadawalin ayyukan da Sakataren shirye-shirye na kasa, Suleiman Argungu ya sanya wa hannu.