Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Rivers, Tonye Cole, ya koka da kame lauyoyinsa uku, inda ya shigar da kara a kotun sauraron kararrakin zabe domin kalubalantar zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, kamar yadda Punch ta rawaito.
Cole ya yi zargin cewa jami’an dake goyon bayan jam’iyyar su biyar an kame su.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP Ta Yi Allah-Wadai Kan Kame Da Tsare Mambobinta A Jihar Kebbi
An tattaro cewa an kama lauyoyin da ke aiki a zauren wani babban lauyan Najeriya, Tuduru Ede a daren Juma’a, a wani otal da suka sauka a Fatakwal.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Kamen dai ya zo ne sa’o’i 48 bayan da Cole ya jagoranci tawagar zartarwar jam’iyyar zuwa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa domin nuna rashin amincewarsu da kin sakin kwafin takardun da aka yi amfani da su a lokacin zaben, wadanda za su taimaka wa jam’iyyar zuwa gaban kotun.
Da yake tabbatar da kamun ga manema labarai a Fatakwal, a ranar Asabar, Cole ya bayyana faruwar lamarin a matsayin tada zaune tsaye, inda ya ce jami’ansu sun kwashe kayan lauyoyin.
Da yake ba da labarin faruwar lamarin, ya ce, “Da safiyar yau ne aka tashe ni tare da buga waya da misalin karfe 7 na safe, cewa an kama lauyoyinmu da ma’aikatan da ke goyon bayanmu aka dauke su daga otal din da suka sauka.
“A lokacin da na garzaya zuwa otal din, sun riga sun tafi.
“An gaya min an kai su sashin leken asiri da sa ido a Ogbunabali (dake Fatakwal).
“Ni da wakilin jam’iyyar da lauyoyinmu muka je can, aka tsare mu sama da awa daya, ba mu gansu ba, sai aka ce an mayar da su sashin binciken manyan laifuka na jiha.
“Ban taba jin an kama lauyoyin da suka shirya takardar koke da ya kaure da lokaci ba. Abin da ya fi damun mu shi ne, an ɗauke duk shaidarmu.
Yanzu, za mu iya amincewa da wannan shaidar idan muka dawo da ita? Lauyoyin suna rubuta takaitaccen bayani kafin a tafi da su. Yanzu, ‘yan adawa sun san ainihin abin da muke so mu yi jayayya. Ina cikin kaduwa,” in ji shi.
Yayin da yake tabbatar da cewa kamen ba zai tsaya ba, ya dage, “Ba zan bar wannan wurin ba a yau har sai an sake su.
Waɗannan lauyoyi ne bisa doka suna shirya kokensu. Ba za mu iya zuwa kotun ba mu gaya musu saboda an kama lauyoyinmu,” dan siyasar ya koka.
Cole ya nuna cewa jihar Ribas lamari ne na musamman, yana mai cewa, “Ba za a iya ci gaba da amfani da ‘yan sanda ba.
“Ina jin ana amfani da ‘yan sanda wajen yi mana zagon kasa. Mun riga mun samu shaidar da aka yi amfani da ‘yan sanda wajen sace kayan zabe a ranar zabe. Dole ne Sufeto Janar na ‘yan sanda ya kira su domin ya ba su umarni,”.
Shi ma da yake nasa jawabin, babban lauyan jam’iyyar APC da ‘yan takararta, Tuduru Ede, SAN, ya ce ba a taba jin ‘yan sanda sun bari a yi amfani da su ba.
Ede ya ce, “Duk a hanyar da za a binne koke. Sun kwashe dukkan takardun EC8 da kwafin sakamakon zaben da muka tattara daga wakilan.
Muna rokon a sako duk wadanda aka kama. Mun yi imanin cewa ma’aikatan otal din sun yi sulhu da zaman da muka yi a wurin,” inji shi.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko ya ci tura saboda ba a iya samunta a waya ba, har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Har yanzu bata amsa sakon da aka tura mata ta wayarta ba.
A wani labarin kuma, Murnar Cin Zabe: Shugabannin Wasu Kasashe Biyu Sun Taya Tinubu Murnar Lashe Zabe
Shugaban ƙasar Cuba, Muguel Diaz-Canel da takwaran sa na ƙasar Nicaragua, Daniel Ortega, sun taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasan Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bisa nasarar da ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023. Rahoton Vanguard
Wata sanarwa da hadimin Tinubu kan harkokin watsa labarai, Tunde Rahman, ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana saƙonnin taya murnar shugabannin ƙasashen biyu ya iso ne a wasiƙu daban-daban.