- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci wasu shugabannin Afirka biyar don bude matatar mai ta Dongote mafi girma a Afirka.
- Bude matatar mai ta Dangote zai fitar da Najeriya daga kasuwar shigo da mai da kawo karshen karancin mai.
- Matatar mai mallakin hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote, zata iya Samar da kashi 100% na abin da Najeriya ke bukata na dukkan kayan da aka tace.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, Faure Gnassingbe na Togo, Mahamat Deby na Chadi, Macky Sall na Senegal da kuma Mohamed Bazoum na Nijar za su bude matatar mai ta Dongote mafi girma a Afirka.
Har ila yau, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai halarci bikin, kuma shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame, wanda ba zai halarta a zahiri, zai gabatar da sakon fatan alheri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kada Ku Yanke Mani Hukunci Dai-Dai da Lokacin Da Ina Minista – Akpabio
Ana sa ran taron da za a yi a baya zai kawo sauyi a harkar man fetur da iskar gas a Najeriya.
DAILY POST ta yi wani duba na irin fa’idojin da Najeriya zata samu da suka hada da fitar da ita daga kasuwar shigo da mai da kawo karshen karancin mai a kasar.
Sabuwar matatar mai mallakin hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote, zata iya Samar da kashi 100% na abin da Najeriya ke bukata na dukkan kayan da aka tace.
Zata samar da (Man fetur, lita miliyan 53 a rana, Diesel lita miliyan 34 a rana, kanazir lita miliyan 10 a rana, da mai sufurin jiragen sama lita miliyan 2 a kowace rana,sannan kuma suna da rarar kowane ɗayan waɗannan samfuran don fitarwa.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, dukkan gwamnonin jihohi 36 da akasarin zababbun gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisar dattawa, da shugabannin masana’antu a Najeriya da sauran su daga wajen kasar, ‘yan kasuwar man fetur na duniya, manyan bankunan kasa da kasa, da hukumomin kasa da kasa da dama sun nuna shirinsu na halartar bikin.
A wani labarin kuma, Tafaru Ta Kare: Likitocin Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Gargadi
Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta umurci mambobinta da su koma bakin aiki a yau (Litinin)
Sai dai NARD ta ce za ta sake duba yajin aikin nan da makonni biyu masu zuwa muddin aka samu tangarda.
Shugaban kungiyar, Dakta Emeka Orji ya ce an dakatar da yajin aikin daga karfe 8 na safiyar ranar Litinin.