- Hukumar ICPC, ta gurfanar da wani Umar Abubakar a gaban kuliya, bisa laifukan da suka shafi zunzurutun zamba.
- Gurfanar da Abubakar ya biyo bayan yiwa wanda abin ya shafa alkawarin zai taimaka masa wajen samar masa da aiki tare da ICPC.
- Alkalin kotun ta bayar da belin wanda ake tuhuma a kan kudi Naira Dubu Dari Biyu (N200,000:00)
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta da sauran laifuka masu alaka ICPC, ta gurfanar da wani Umar Abubakar a gaban kuliya, bisa laifukan da suka shafi jabun takardu, zamba da kuma aikin yi,Vanguard ta rawaito.
Abubakar ya tsaya ne a gaban mai shari’a Hafsat Abdulrahman ta babbar kotun jihar Adamawa dake zaune a Yola babban birnin jihar.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Kudirin Dokar Albarkatun Ruwa
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua ya fitar a Abuja ranar Talata.
Hukumar a tuhuma mai lamba: HC/ADSY/127C/2022, ta zargi wanda ake kara da laifin karbar kudi Naira Dubu Dari Biyu (N200,000) daga hannun wani ma’aikaci da ba a taba tsammani ba, tare da yiwa wanda abin ya shafa alkawarin zai taimaka masa wajen samar masa da aiki tare da ICPC.
Daga nan ne alkalin kotun ta bayar da belin wanda ake tuhuma a kan kudi Naira Dubu Dari Biyu (N200,000:00) da kuma wanda zai tsaya masa a karkashin ikon kotun.
An dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Yuni, 2023 domin fara shari’ar.
A wani labarin kuma,Taleko Ta Koma: Wani Gwamna Ya Dakatar Da Daukar Ma’aikatan Gwamnati
Gwamnan Cross Rivers Sanata Bassey Otu ya bayar da umarnin dakatar da daukar ma’aikata a jihar.
An umurci dukkan ma’aikatan jihar da su mika kansu ga tantancewa da kuma takardun shaida.
Tsohon gwamnan jihar Ben Ayade a karshen gwamnatinsa ya dage takunkumin da ya kakabawa aiki da kuma karin girma.
Gwamnan jihar Cross Rivers Sanata Bassey Otu ya bayar da umarnin dakatar da daukar ma’aikatan da ake ci gaba da yi a ma’aikatun gwamnati har sai an yi wata sanarwa nan gaba.