Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Katsina game da asarar rayuka da dukiyoyi da rashin tsaro da jihar ke fama da shi.
Sarkin ya yi jajen ne a ranar Laraba, a fadar gwamnatin jihar Katsina, yayin da ya kai wa Gwamna Aminu Bello Masari ziyarar ban girma.
“Maƙasudin kawo wannan ziyara shi ne jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Katsina sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da a bayan-bayan nan suka zamto ruwan dare a jihar.
https://dimokuradiyya.com.ng/matsalar-tsaro-yadda-matasa-suka-yi-zanga-zanga-a-jihar-katsina/
“Duk abin da ya shafi Katsina mu ma ya shafe mu, kuma muna tarayya da su cikin duk wata damuwarsu domin da mu da su duk abu ɗaya ne.
“Muna so mu tabbatar wa gwamnati da al’ummar Katsina cewa, muna yi muku addu’a tamkar yadda muke yi wa kawunanmu. Muna rokon Allah Ya kawo karshen wadannan musibu kuma Ya dawo mana da zaman lafiya da aminci a kasarmu”, inji Sarin Kano.