Gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da tawagar su sun kai ziyara Gidan Murtala domin duba sabuwar Ma’aikatar Addinai, da kuma duba tamkunan ruwa guda 15 na wanke hannu domin kare kai daga kamuwa da cutar corona wanda gidauniyar Khalifa Dankadai KDC ta bawa gwamnati gudunmawa domin rabawa ga tsangayu a jihar Kano.
Haka kuma gwamna Ganduje ya gana da Alarammomi guda 60 da gwamnatinsa ta ɗauka aiki kwanan nan domin tura su manyan makarantun tsangaya da gwamnatin ta samar, ƙarƙashin jagorancin ma’aikatar ilimi.
Mai bai wa gwamna shawara akan kafar yaɗa labarai, Malam Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyanawa manema labarai a yau Litinin da suke ƙaddamar da buɗe ma’aikatar.