Dandazon magoya bayan tsohon shugaban mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya Dakta Obadiah Mailafia sun yi wa ofishin hukumar DSS na Jos tsinke domin taya sa murna, bayan da hukumar ta sake shi.
Magoya bayan sun ta raira waƙoƙin goyon bayan a farfajiyar ofishin hukumar ta DSS.
Sai dai Mailafia ya yi fatan cewa wannan shi ne karo na ƙarshe da hukumar zata gayyatarsa domin sake amsa wasu tambayoyin.
Idan ba a manta ba jaridar Punch ta rawaito cewa hukumar DSS dake Jos ta sake gayyatar Mailafia zuwa ofishinta a ranar Litinin domin sake amsa wasu tambayoyi.
Wannan shi ne zuwan Mailafia ofishin hukumar a karo na uku tun bayan hirar da yayi a gidan rediyo.
Mailafia ya bayyana a ofishin hukumar ta DSS da misalin ƙarfe 11 na safe, kuma ya samu rakiyar matarsa Magret sai kuma lauyansa Yakubu Bawa da wasu sauran mutane.
Hukumar bata sallame sa sai bayan ƙarfe 2:55 na yamma.
Sai dai da yake yiwa magoya bayansa jawabi ya yi alawadai da sake gayyatarsa da hukumar ta yi.