Hukumar karɓar koke-koke da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta karɓo kuɗi har miliyan bakwai da aka karkatar da su a ma’aikatar noma ta jihar Kano.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Muhyi ya ce, ma’aikatar Noman na karɓar kuɗaɗen haraji a hannun manoma domin ba su damar yin noma a filayen noma na gwamnatin Kano, sai dai kuma ana karkatar da kuɗaɗen.
Ya ƙara da cewa, baya ga miliyan bakwai da suka karɓo, yanzu haka su na tsaka da bincike kan wasu kuɗaɗen har sama da miliyan bakwai da aka yi zargin su ma an karkatar da su a ma’aikatar.
Yace, wannan ya saɓawa sashe na 26 na dokar hukumar a don haka ya zama dole su ɗauki mataki a kai.
Muhyi ya ce, yanzu haka suna ci gaba da bincike kuma har sun gayyaci manyan ma’aikata a ma’aikatar noman tun daga kan babban sakatare har zuwa daraktoci.
A ƙarshe ya ce, binciken su zuwa yanzu bai nuna cewa akwai hannun kwamishinan noma na Kano ba, wanda shi ne mataimakin gwamnan Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna.