Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki, Tolu Bankole, ya goyi bayan kiran aiwatar da nadin kashi 10 cikin 100 a ma’aikatu da hukumomin tarayya ga nakasassu kamar yadda dokar hana wariya ta 2018 ta tanada
Bankole, wanda shi ne shugaban nakasassu na kasa a jam’iyyar APC, ya mayar da martani ga bukatar da aka gabatar a zauren majalisar wakilai a ranar Alhamis inji jaridar PUNCH
A ranar Alhamis ne majalisar ta bukaci a aiwatar da kashi 10 cikin 100 na kason aikin yi ga nakasassu ba tare da bata lokaci ba
Rokon ya biyo bayan kudirin da dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Kosofe ta Legas, Kafilat Ogbara ya gabatar
KARANTA NANNSCDC Ta Kame Wasu Barayi Da Suka Kware Wajen Lalata Husumiyar Sadarwa
Ogbara ya jaddada cewa an zartar da dokar nuna wariya ga PWDs Prohibition Act 2018 don tabbatar da kiyaye haƙƙinsu
Don haka Majalisar Wakilai ta bukaci Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, da ya umurci Shugaban Ma’aikata na Tarayya da kuma MDAs
Da su yi aiki da tanadin sashe na 29 na dokar nuna wariya ta 2018 ta hanyar sanya dokar wariya. akwai alƙawura
Ya ce, basu suka zabi zama nakasassu ba kuma babu wanda yafi karfin ya zama nakasasshe,saboda haka suna bukatar kulawa ta musamman
Ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga jiga-jigan Sanatoci a zauren majalisar wakilai da daukacin Majalisar Dokokin Jihohi da su bayar da gudumawarsu
Wajen ganin an Nawa nakasassu manyan mukamai a cikin sabuwar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu
A WANI LABARIN KUMA
Ku Kai Karar Bankinku Idan Kudinku Suka Makale-CBN Ga Yan Najeriya
Babban bankin hada hadar kudi ta Najeriya Central Bank Of Nigeria ya tabbatar da duk wani wanda kufinsa suka makale a cikin asusun bankinsa da ya gaggauta kai karar bankin da yake amfani dashi
Hakan zai tabbatar da hakkin masu amfani da bankuna suke dashi wajen gudanar da harkokin