Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce masu amfani da kudi na da ‘yancin kai rahoto ga bankunan su idan wata matsalar ta taso
Mista Elachi Samuel na Sashen Kare hakkokan abokan cinikayya ne ya bayyana haka a Bauchi yayin bikin baje koli na bankin don fadakar da masu ruwa da tsaki da manoma kan wasu hanyoyin biyan kudi domin zurfafa hada-hadar kudi
Da yake magana game da hakki da alhakin masu amfani da kuɗi,Mr Elachi Samuel yace yana cikin haƙƙin ku ajiye duk wani rakwad na kudin da kuka tura ko aka turo muku
Wannan zai ba ku damar sanin cewa ba a gajarta ku ko yaudara ba. Masu amfani da kudi dole ne su san cewa suna da ‘yancin kai rahoton bankunan su ga CBN kan hada-hadar da ba a warware ba
Idan kuka kawo mana rahoton matsalar, za mu duba lamarin, mu tabbatar mun duba kuma munyi aiki akanshi ya fadawa jaridar Daily Post
A tsakanin 20 ga Mayu, 2013 zuwa 20 ga Mayu, 2023, mun sami damar dawo da Naira biliyan 115.45 na cinikin banki da basu samu kammaluwa ba,ya kuma kara da cewa mun sami korafe-korafe 35,453. Mun warware 33,437
Ya kuma ja hankalin kungiyoyin manoma da su rungumi manufofin cibiyar hada-hadar kudi ta e-Naira domin itace hanya mafi sauki ta hada hadar kudi nan gaba
A WANI LABARIN KUMA
William Saliba Ya Kara Kwantiragin Shekaru 5 A Arsenal
William Saliba ya rattaba hannu kan wani sabon kwantiragin da zai bar shi a Arsenal har tsawon shekaru biyar
Arsenal na fatan sun kara karfafa tawagar yan wasanta domin tunkarar kakar badi, ganin cewar a bana sun rasa lashe wani Kofi a Turai abinda ya baya ran magoya bayan Kungiyar dake London