Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya NSCDC ta jihar Borno ta samu nasarar kame wasu mutane 27 da ake zargi da aikata maban-bantan laifuka, wanda shida daga cikin su sun kasance masu lalata husumiyar turakun sadarwa, Vanguard ta rahoto.
Da yake jawabi ga manema labarai a Maiduguri a ranar Juma’a, Kwamandan jihar, Mista Musa Farouk, ya ce an kama barayin shida ne a kauyen Shiki da ke karamar hukumar Chibok, inda suka lalata wata katafariyar husumiyar kamfanin NITEL.
KARANTA WANNAN: Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabon Nadi A Gwamnatin Sa
“Mun samu sahihin bayani a ranar 25 ga watan Yuni cewa ana lalata wani ginin hasumiyar sadarwa.
“Bayan samun wannan bayanin, na umarci jami’ai na da ke cikin wannan wurin da su kasance kan wasan don kame masu laifin.
“Sun je wurin ne a kauyen Shiki da ke Chibok,” in ji Farouk.
Ya bayyana cewa wadanda ake zargin su shida da aka kama sunkasance direbobin manyan motoci uku ne cike makil da wasu sassan katafariyar husumiyar da aka lalata, yayin da wadanda suka dauke su aiki na nan a hannun su.
Kwamandan ya kuma gabatar da wasu da ake zargi da lalata igiyoyin wutar lantarki, kayayyakin gini da kuma wasu bata gari da ke ta’addanci da karbar kudade daga hannun jama’a.
Ya nuna damuwarsa kan yadda matasa ke shiga cikin aikata miyagun laifuka, ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki musamman iyaye da malaman addini da su gaggauta magance matsalar da ke tada hankali.
Yayin da yake nanata kudurin rundunar na sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare wasu muhimman kadarori, Farouk ya yabawa kwamandan rundunar da kuma Gwamna Babagana Zulum na Borno bisa irin goyon bayan da suke baiwa rundunar.
A wani labarin kuma,Wani Gwamna Ya Rantsar Da Kwamishinoni
Gwamnan Abia, Dakta Alex Otti, a ranar Juma’a, ya rantsar da kwamishinoni 16 da majalisar dokokin jihar ta wanke su tare da raba musu mukamai.
Wadanda aka rantsar sun hada da Barista Ikechukwu Uwanna (Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a,), Farfesa Monica Ironkwe (Ma’aikatar Noma), Kingsley Anosike (Kasafin kudi da tsare-tsare), Farfesa Misis Uche Eme Uche (Ma’aikatar Ilimi), Philemon Asonye Ogbonna (Ma’aikatar Tsara Muhalli da Birane).