Hukumar kiyaye hadurra ta kasa, FRSC reshen jihar Kwara, ta ce mutum 253 ne suka rasa rayukansu sakamakon hadurra a tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban 2020.
Kwamandan hukumar, Jonathan Owoade, ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Talata a Ilorin.
Har wala yau ya kara da cewa; a tsakanin wadannan watannin, an yi hadurra 321, inda ya rutsa da mutum 2,399 a yayin da mutum 1,103 suka raunata.