Akalla mutane 349 aka kashe a sanadiyar munanen hare-haren da aka kaddamar a cikin watan Nuwamban da ya gabata a sassan Najeriya kamar yadda wani rahoto da kungiyar ‘Nigeria Mourns’ ta fitar ke cewa.
Gidan rediyon Faransa ya labarto cewa; rahotan mai taken “ Munanan aukuwa” ya yi nazari kan kashe-kashen da aka samu a sassan Najeriya a cikin watan Nuwamba kadai, kuma kingiyar ta Nigeria Mourns ta tattara alkalumanta ne daga jaridu da kuma majiyoyin iyalan mamatan.
Kungiyar ta kewaya jihohin Najeriya 23 domin tattara alkaluman.
Rahotan ya nuna cewa, fararen hula 309 aka kashe daga cikin adadin, yayin da aka hallaka jami’an tsaro 40.
Kazalika rahoton ya nuna cewa, an yi garkuwa da mutane 290 a cikin watan na Nuwamba kadai.
Jihar Borno ke kan gaba wajen yawan asarar rayukan al’umma a cikin watan kamar yadda alkaluman mamatan suka nuna.
Ga cikakkun alkaluman da kungiyar ta fitar:
Borno – 162, Edo – 57, Kaduna – 55, Katsina -12, Delta – 11, Zamfara – 10, Oyo – 5, Ondo – 5, Enugu – 4, Kogi -3, Kano – 3, Ekiti – 3, Adamawa – 3, Bayelsa – 3, Cross River – 2, Nasarawa – 2, Niger – 2, Rivers – 2, FCT – 1, Akwa Ibom – 1, Ebonyi – 1, Ogun – 1 and Sokoto – 1.