Cibiyar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC a ranar Juma’a a cikin kididdigar da ta fitar ta nuna cewa mutum 1,689 ne suka warke daga cutar korona a rana guda a Nijeriya.
NCDC har wala yau ta ce a ranar ta Juma’a, an samu sabbin mutum 329 da suka kamu da cutar, sannan kuma cutar ta kashe mutum bakwai.
Baki daya a Nijeriya mutum 48,445 ne suka kamu da wannan cuta inda kuma tuni aka sallami mutum 35,998.A yayin da kuma mutum 973 ne suka mutu sakamakon cutar a Nijeriya.