A irin wannan rana ta 9 ga watan Oktoba na shekarar 1994 aka haifi shahararriyar ‘yar wasan Najeriya wato Asisat Oshoala inda za a iya cewa yau ce takeyin murnar bikin zagayowar ranar haihuwarta kenan, a yanzu dai tana da shekaru 26 kenan cif-cif a duniya.
An haifeta a jahar Lagos a garin Ikorodu inda take da tsawon mita 1.73 kuma ita tana buga wasa a matsayin maijefa ƙwallo wato ‘yar wasan gaba kenan. Ta fara buga wasanta a matsayinta na matashiyar ‘yar wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta F/c Robo.
A halin yanzu tana fafata wasanta a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona dake ƙasar Andalus inda taje ƙungiyar a shekarar data gabata ta 2019 inda ta buga wasanni 19 ta jefa ƙwallaye guda 20. Tana sanya riga mai lamba 20 a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Barcelona a halin yanzu.
Sai dai kafin ta moma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta fafata wasanni a ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da suka haɗar da F/C Robo da Rivers Angels da Liverpool Ladies da Arsenal Ladies da Dalian Quanjian F.C. da kuma ƙungiyar datake a halin yanzu wato Barcelona.
A matakin ƙasa kuwa ta bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafan mata ta Super Eagles wasanni 17 inda ta jefa ƙwallaye guda 11. Haka zalika ta wakilci Najeriya a gasa daban-daban kuma ‘yar wasa ce mai ƙwazo.
Oshoala ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar wasa ta nahiyar Afrika har sau 4 a tarihi, sannan ta lashe kyautar gwarzuwa ‘yar wasa ta kafar yaɗa labarai ta BBC a shekarar 2015. Sannan itace ‘yar wasan Afrika ta farko data buga wasan ƙarshe na gasar zakarun turai ta jefa ƙwallo a wasan ƙarshen.