Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci a gudanar da bincike kan yawaitar mutuwar a Kano, inda ta ce akwai bukatar shugaban kasa ya kai ziyara a can.
Jami’yyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Kakakinta, Kola Ologbondiyan ya fitar, inda ta ce rahotanni sun nuna cewa daruruwan al’umma ne suka rasu cikin mako guda a Kano ba tare da sannin abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsu ba.
Kiran na zuwa ne a lokacin da ake samu rahotanni masu cin karo da juna kan abin da ya janyo mutuwar al’umma a Kano a lokacin da ake fama da annobar cutar Korona.
Har yanzu shugaban kasa Buhari bai yi jawabi a hukumance ba dangane da batun. A yayin da gwamnatin jihar Kano suka alakanta yawaitar mace-macen da haduwar cututtuka daban-daban da suka hada da Maleriya, typhoid da sauran su.