Wanu ɗan sanda ya tafi da zuciyar mutane da dama bayan yayi wani abin alkhairi ga wani yaro mai taɓin hankali.
A cikin bidiyon mai taɓa zuciya wanda aka sanya a manhajar TikTok, an nuna ɗan sandan yana zaune kusa da yaron inda yake ta kallon sa cike da tsantsar kulawa a fuskar sa. Rahoton jaridar Legit.ng ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Zaɓen 2023: Kwankwaso ya samo koma baya, wani babban jigo da magoya bayan sa sun fice daga NNPP
A cikin sauran bidiyon kuma, ɗan sandan ya samo almakashi inda yayi wa yaron mai lallurar taɓin hankali aski a wajen, kafin daga bisani ya kai shi wani waje inda yayi masa wanka da kan sa.
Nan da nan kamannin yaron suka sauya saboda kulawar da ɗan sandan nan ya bashi.
Daga nan sai aka nuna ɗan sandan ya ɗora hannun sa akan kafaɗar yaron.
Ku kalli bidiyon a nan
Bidiyon ya ɗauki hankulan mutane sosai inda suka yi ta yabawa ɗan sandan bisa wannan kulawa da ya nunawa yaron.
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda jaridar Dimokuradiyya ta tattaro:
linmakafui ya rubuta:
“Allah yayi albarka sannan ya baka tsawon rai ɗan sanda.”
lovely Baby ta rubuta:
“Dan Allah akwai wanda zai samo min lambar wayar ɗan sandan nan, ina son nayi masa alheri.”
gabrieloduro663 ya rubuta:
“Wannan shine abinda nake son na zama nan gaba. Allah ka taimake ni.”
Kotu Ta Umurci Biyan Diyyar N1.5m Ga Wata Mata Bayan An Yi Mata Sharrin Maita
A wani labarin na daban kuma, wata mata ta samu diyyar N1.5m bayan an yi mata ƙazafin maita.
Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta babbar kotun jihar Kano, ta bayar da umurnin wasu mutum biyar su biya tarar N1.5m ga wata mata, Sahura Suleiman, bayan sun kirata da mayya.
Majiyar mu ta tabbatar da cewa, Sahura ta zargi mutum shidan da gaya mata kalamai masu muni waɗanda suka haɗa da, mayya, munafuka da kuma shegiya.
Waɗanda ake ƙarar dai sune, abi’u Wise, Talatu Salisu, Ummi Tasi’u, Mariya Musa, Nauwara Salisu, Aisar Gandu, Baba Umaru da wani boka (Suwidi Habibu).