Ranar Litinin, 23 ga watan Janairun 2023, Allah ya yi wa Jarumi kuma furodusan masana’antar Kannywood, Abdulwahab Awarwasa, rasuwa.
Bayan ya kwashe tsawon lokaci kamar yadda Mujallar Fim ta bayyana, jarumin ya kwanta dama.
KU KARANTA: Matashi ya halaka kishiyar mahaifiyarsa da ‘yarta
Awarwasa asali dan unguwar Fagge ne da ke cikin garin Kano, kuma ya dade yana jan zarensa a masana’antar inda yake fitowa a matsayin dan daba.
Yaron Ali Nuhu ne kuma furodusa ne wanda ya shirya finafinai da dama tsawon lokaci. Wata majiyar ta kusa da marigayin ta shaida yadda ya dade yana fama da ciwo kafin Allah ya dauki ransa.
Marigayin magidanci ne wanda yake da mata daya da yara uku. Mutuwarsa ta zo ne bayan kwanaki kadan da rasuwar fitaccen jarumin barkwanci, Kamal Aboki.
Tabbas mutuwar ta taba jarumai da dama na masana’antar inda suka dinga wallafa hotunansu tare da shi suna yi masa fatan rahama.