Daga Mukhtar Yakubu.
Tsohon jarumi a masana’antar fina-finai ta Kannywood Shu’aibu Idris Lilisko, ya bayyana wargajewar da masana’antar ta yi a yanzu da cewar, hakan ya samo asali ne da tun farko ita harkar ta fim ba ta samu wani kyakkyawan tsarin da zai tafiyar da ita ba, don haka da tafiya ta yi tafiya aka samu shigowar mutane da yawa, sai kuma ta cika ta batse wanda hakan ya jawo sanadiyyar wargajewar ta.
Jarumin wanda a shekarun baya kamar shekaru 20 da su ka wuce ya ta ka matsayin da kusan babu wani jarumin da ya kai shi iya rawa, a cikin masana’antar, wanda hakan ta sa ya yi fice da babu wani jarumin da ya kama kafar sa.
Sai dai a yanzu da tafiya ta yi tafiya Shu’aibu Idris Lilisko ya bayyana wa wakilin mu cewar “mu a yanzu zamani ya tafi da mu, don haka sai dai mu zama yan kallo. Domin kuwa a yanzu da yara su ka mamaye harkar, kuma babu wani tsari da aka yi mata wadda hakan ya bai wa kowa damar shigowa ta in da ya ga dama, don haka sai dai abin da aka gani.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun karyata rahoton kai wa Sarkin Kano harin.
Ya cigaba da cewar” a baya mu ne ku ke fitowa a matsayin jarumai, don kuwa a lokacin in dai za a fadi sunan jarumai a masana’antar idan ban zo na biyu ba to zan zo na uku, kuma ina fitowa a babban jarumi saboda in dai rawa ce to babu wanda ya Isa ya ja da ni don duk wata rawa da a ke yi a lokacin ko ta Gargajiya ko ta zamani, to ni nake koyar da ita, amma yanzu da zamani ya cinye mu na koma sai dai na fito a matsayin Dan Sanda. Amma dai babbar matsalar da take damun masana’antar wadda har ta kai da wargajewa, rashin tsarin shugabanci, wannan ta sa kowa ya ke yin abin da ya ga dama, don haka a yanzu harkar fim ta kai matsayin da idan aka ce za a gyara ta sai ka rasa ta ina za a fara gyaran, don haka a yanzu dai harkar ta wargaje gyaran ta kuma sai dai abin da Allah ya yi, ban ce ba za ta gyaru ba, Amma dai abu ne mai wahalar gaske. ”
Daga karshe ya yi fatan Allah ya kawo wa harkar mafita.