Mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United wato Ole Gunner Solskjaer ya bayyana dalilin dayasa bai fito da Poul Pogba ba a ‘yan 11 na farko da suka fuskanci ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle ba a wasan mako na 5 na gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila.
Ole ya bayyana cewar dalilin dayasa baifito da Pogba ba a makon daya gabata ‘yan wasa sun bugawa ƙasashensu na haihuwa wasannin share fage da kuma wasannin sada zumunta wanda hakan ya sanya wasu ‘yan wasan jin ciwo.
Shima dai Pogba yaki rauni a kuturinsa a wasan da ƙasar Faransa ta fafata inda hakan ya sanya Pogba akemasa magani, wanda ko a kiya Pogba zai iya buga wasan amma kuma ganin yadda akwai wasannin masu zafi a gaban Manchester yasa ba a aakashiba.
A wasan na jiya dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta fusata inda ta huce akan Newcastle inda ta ragargazata daci 4 da 1 har gida. Idan ba’a manta ba a makon daya gabata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham ta rugurguza Manchester United har filin wasa na Old Trafford daci 6 da 1.
A tsakiyar makonnan za a dawo fafata gasar zakrun nahiyar turai inda itama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United zata buga wannan gasa amma kuma a kakar wasan data gabata bata buga gasar ba amma ta buga gasar Europa League inda Sevella ta koreta a wasan kusa dana ƙarshe.