A karon farko an dakatar da gasar Golf ta ƙasar Australia inda aka bayyana cewar baza ayi wannan gasa a wannan shekarar ta bana ba duba da irin yadda aka tsinci kai daga shekarar data gabata zuwa yanzu ganin yadda duniyar take a rikice sabo da cutar nan ta Coronavirus data addabi duniya.
An dakatar da wannan wasan na Golf ne sabo da annobar cutar Coronavirus wadda har yanzu akwai ragowarta knda takeci gaba da kama mutane musamman a nahiyar turai inda ko ayanzu akwai mutanen da suke a killace.
Sakamakon wannan cutar ta Coronavirus tasa aka dakatar da kowanne wasanni a nahiyoyi daban-daban inda za a iya cewa tsirarin ƙasashe ne basu dakatar da wasanninsu ba kuma har ‘yan kallo suna shiga su kalli wasannin nasu idan suna gudanar dasu kuma a haka suka kammala wasannin nasu.
Amma kuma daga bisani da cutar tayi sauƙi an dawo anci gaba da fafata wasanni amma kuma ba tare da ‘yan kallo ba inda ahaka akai ta fafata wasanni daban-daban kuma aka ƙarasa wasannin ahakan inda ayanzu anfara yin wasu wasannin ba tare da ‘yan kallo ba kama daga wasannin ƙwallon ƙafa dama sauran wasanni gabaɗaya.
Itadai wannan gasa ta Golf shekaru 105 ana gudanar da ita amma ba’a taɓa dakatar da ita ba sai a wannan lokacin cutar ta Coronavirus. Idan za a iya tunawa an dakatar da kusan kowacce gasa ciki harda gasar guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympics daza ayi a can ƙasar Japan.
Ayanzu dai ta tabbata cewa baza a gudanar da wannan gasa ba ta Golf a wannan shekarar ta 2020 inda aka bayyana cewar sai a shekara mai kamawa ta 2021 za a gudanar da gasar, ita dai wannan gasa tana ƙayatarwa sosai da sosai ganin yadda ake kallonta a duniya duba da cewar gasa ce mai cike da tarihi.