Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana ci gaba da shigo da man fetur a Najeriya, duk da cewa kasar na daya daga cikin manyan kasashe masu arzikin danyen mai a duniya, a matsayin abin kunya.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Obaseki ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a Ewohimi, na karamar hukumar Esan ta kudu maso gabas ta jihar Edo, a wajen taron bikin cika shekaru 10 da nada Chief Jeremiah Ighodalo, mahaifin shugaban bankin Sterling Plc, Dr. Asue Ighodalo hawa kan karagar mulki.
Ya ce “ci gaba da shigo da man fetur cikin kasar nan, abin kunya ne ga Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin Karin Kudin Data Dana Kiran Waya— Pantami
“A matsayinta na daya daga cikin manyan masu samar da danyen man fetur a Nahiyar Afrika, shigo da mai cikin kasar nan. Abin kunya ne, kuma har yanzu muna shigo da mai”
A matsayinmu na kasar da take da mai, bai kamata mu rika shigo da man fetur daga kasashen waje a wannan lokaci ma rayuwarmu ba. Abin kunya ne na rashin kishin ƙasa, idan na aro daga kalmomin marubucin Najeriya, Chimamanda Adiche,” in ji shi.
Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, a lokacin da yake magana a kan matatar Man sa, ya ce da fatan kamfanin zai fara aiki da samar da Man fetur nan da shekarar 2023 mai zuwa.
Ya yi bayanin cewa matatar man za ta iya samar da albarkatun man fetur ga daukacin Najeriya da wasu sassan yammacin Afirka da tsakiyar Afirka nan da shekarar 2023,.
Ya ce yana da kwarin gwiwar cewa matatar man za ta magance shigo da man cikin Kasar nan, da zarar ta fara aiki.
A WANI LAAMBARIN KUMA: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Hallaka Mutum 5 A Jihar Jigawa
Rahotanni sun ce mutane 5 ne suka mutu yayin da aka ceto wasu hudu daga wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Gwaram da ke jihar Jigawa.
Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a kauyen Martaba a lokacin da fasinjojin ke komawa