Shugaban kasa Manjo Janar Buhari ya aika da sunan mai shari’a Dongban Mensem zuwa majalisar Dattawa domin tabbatar da ita a matsayin shugabar kotun daukaka karar Nijeriya.
Wannan ya sanya JARIDAR MADUBI, ta bibiyi rayuwarta domin gano wadansu abubuwa dangane da ita.
Wadannan sune abubuwa 10 da ba ku sani ba dangane da ita:
1- Cikakken sunanta shi ne Monica Bolna’an Dongban-Mensem
2- Mai shari’a Dongban-Mensem ‘ya ce ga Mai shari’a M. B. Douglas-Mensem, Alkali (mai ritaya) a kotun daukaka kara.
3- Ta fito ne daga karamar hukumar Shendam ta jihar Filato.
4- Mensem tana da ‘ya’ya hudu (daya ya rasu) tare da jikoki guda hudu.
5- Ta yi digirinta na farko da na biyu LL.B da LL.M a fannin karatun Laya a jami’ar Ahmadu Bello University (ABU) dake Zariya, sannan ta yi PGD dinta daga ‘Institute of Advanced Legal Studies, University dake Landan (Russel Square – London).’
6- Mai shari’a Dongban-Mensem tana son rubutun, karatu da kuma wasan golf. Tana jindadin aiki da yara, mata da kuma tsofaffi.
7- Sakamakon bakin cikin rashin danta da ta yi mai suna Prince Samson Kwapda’as Dongban, ta kirkiri kungiyar kiyaye hadurra ta mai suna Kwapda’as Road Safety Demand (KRSD), wanda kungiyarta ta shahara a Nijeriya.
8- Mai Shari’a Mensem tana daya daga cikin ma’aikatan shari’a masu kwazo. Ya zuwa watan Disamban 2019, tana da shari’o’i 150 da ta jagoranta, tare da bada gudummawa ga yanke hukunci 100.
9- Mai shari’a Mensem masaniya ce akan dokokin harkar miyagun laifuka, haraji, da kuma kudaden shige da fice na al’umma, dokokin ‘yan majalisu, dokokin mulki, da kuma huldar kasuwancin kasashen waje.
10- Mai Shari’a Dongban-Mensem, duk da ayyukan ofishi da yake gabanta, amma ta kaddamar da littafinta mai taken; ‘The Defendant in 1991.’
Littafin ya yi magana ne akan hakkokin wadanda ake takewa hakki, kuma littafin ya zama madogara ga Lauyoyi da wadanda ba su san hakkinsu ba.