- Shugaban kasa, Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayu a jawabinsa na farko ya sanar da cire tallafin man fetur.
- Da wannan sanarwar, farashin PMS da aka fi sani da man fetur ya yi tashin gwauron zabbi inda ake cefanar dashi kusa naira 700 kan kowacce Lita.
- Kwanaki biyu bayan da Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur NNPCL ya kara farashin Famfo na man Fetur
Shugaban kasa, Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayu, yayin jawabinsa na bude taron ya sanar da cire tallafin man fetur,Punch ta rawaito.
Da wannan sanarwar, farashin PMS da aka fi sani da man fetur ya yi tashin gwauron zabbi a wasu gidajen sayar da man fetur da ya kai Naira 700 kan kowace lita.
KARANTA WANNAN: Cire Tallafi Man Fetur: NUJ Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Marawa NLC Baya
Sabanin yadda hukumar NNPCPL za ta kara farashin man fetur a watan Yuni, amma sun yi hakan ne a ranar 31 ga watan Mayu, kwanaki biyu bayan da Tinubu ya sanar da cire tallafin.
Da yake bayyana dalilin hakan, NNPC, ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2022, gwamnatin tarayya ba ta biya wani tallafi ba, inda ya kara da cewa, ya zuwa watan Maris din shekarar 2023,NNPC na bin gwamnatin tarayya bashin zabar kudi har Naira tiriliyan N2.3trn na tallafin man fetur.
Tare da cire tallafin man fetur, ga abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da NNPCPL da kasuwar mai.
1. Duk da cewa kamfanin na NNPC yana ci gaba da sayar da tsofaffin a jiyayyen mai, kamfanin ya bayyana cewa yana bukatar a sayar da man kan sabon farashi domin samun damar sake dawo da shi.
2. Hukumar NNPCPL ba za ta daina shigo da man fetur cikin kasa kadai ba.
3. Hukumar NNPCL ba za ta daina daidaita farashin man fetur a kasuwa ba. Za a ƙayyade farashin ga mai siyarwa.
4. Sojojin kasuwa ne za su tantance farashin man fetur a kasuwa
5. Hukumomin gwamnati, duk da haka, za su kasance cikin shiri don tabbatar da cewa ba a damfari ‘yan kasa.
A wani labarin kuma, Ku Sanya Bukatun Mutane A Gaba – Gwamnan APC Ya Fadawa ‘Yan Majalisa
Oluwarotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, ya bukaci sabbin ‘yan majalisa da su sanya bukatun al’umma agaba wajen gudanar da ayyukansu.
Gwamnan ya bukaci ‘yan majalisar su dauki nauyin da ke kansu a matsayin hidima ga mutanen da suka zabe su.
Kada ku kasance masu nuna bangaranci da gudanar da ayyukan ku ba tare da wani tsoro, son rai, ko tsangwama ba.