Zango Road dake Daura, unguwar shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta cika da alhini bayan wani Dan unguwar Mai suna Ibrahim Lawal ya rataye kansa.
Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewar Marigayi Ibrahim Lawal ya raye kansa ne da Igiya a wani icce dake kan layin unguwar su.
Mai daukar rahoton cewa yayi, jama’a sun hangoshi yana lilo wuyansa daure da Igiya.
KARANTA:- 2023: Ku gama ficewar ku zuwa APC, hakan ba zai hana mu cin zabe ba, Cewar PDP
Ibrahim Lawal mai kimanin shekaru 40 Kuma ma’aikacin ma’aji a Karamar hukumar Sandamu dake Jahar Katsina.
Yan’uwansa da abokan arziqi na cikin damuwa kan rashin sanin dalilin da ya sanya Marigayi Ibrahim Lawal rataye kansa, Kuma bai bar wani sako ba koda a rubuce lokacin da zai aikata kisan kan.
Wasu dai suna zargin yanayin da ake ciki na rashin kudi ne ya sanya shi hakan, inda kuma wasu suke ganin shaye-shaye ya sanyashi yin hakan.
A lokacin da mai rahotanmu yake zantawa da matar sa Malama Hadiza Chedi, cewa tayi “Mijina na cikin wani yanayi na damuwa tun shekaru sha biyar da ta gabata, kuma ya aikata hakan ne saboda kunci da ya sami kansa a ciki.”
Malama Hadiza tana kuma lokacin da take zantawa da manema labaranmu, muryarta bai cika fitowa sosai ba lokacin da take mana bayani.
Malama Hadiza tace “Munyi aure dashi kimanin shekaru 20 da suka wuce, ya kamu da rashin lafiya amman bamu San katamaiman abunda ke damuwar sa ba, Lokacin da mukaje asibiti wajan likita cemasa yayi ya kamu da zazzabin cizon sauro, baya samun bacci.”
” A lokacin da mahaifiyar ke raye ta kaishi kasar Nijar don maganin gargajiya, amma duk da hakan ba wani sauki.”
“Akwai wata rana da naje suna, munyi dashi zai zo ya dauke ni misalin karfe shida har saida nakai karfe tara bai zoba, dana dawo gida inata buga kofar ba’a bude ba, sai nace da wani ya tsallaka ya bude mani, bayan na shiga sai na sameshi yanata bacci dana tadashi nake tambayar sa lafiya kaketa bacci haka, sai yace lafiya lau.”
“Da dai na matsa masa da tambaya shine yake cemasa wani abokinsa ne ya bashi kwaya.”
“Da muka bincika sai mukaga kwayar tramadol ne kuma ya ruga ya kamu da shanta.”
Hadiza ta cigaba da cewa “Tun lokacin da ya kamu da shan kwayoyin baya son shiga mutane, sai ya dinga ware kansa daban.”
A lokacin da mai rahotanmu yake tambayar ta ko ya kashe kanshi ne saboda talauci cewa tayi “Mijina ma’aikaci ne yana a matakin albashi GL14, kuma dima inada hanyar samu, kai daga ganin gidanmu bazakace akwai yunwa ba, muna rayuwar mu daidai gwargwado.”