Farfesa Kingsley Mohgalu tsohon dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar YPP, ya shawarci gwamnatin tarayya kan yadda zata shawo kan matsalar masu zanga-zangar kafa kasar BIAFRA da ODUDUWA.
Ya kuma nuna rashin jindadinsa kan kama shugaban zanga-zangar kafa kasar BIAFRA wato Nnamdi Kanu, da kuma harin da aka kaima mai jogorantar zanga-zangar kafa kasar ODUDUWA Sunday Iboho.
Kamar yadda yace ” Matakin shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kama Nnamdi Kanu da Sunday Iboho bai dace ba.”
KARANTA:- Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun sake yin garkuwa da Mutum 13 a Kaduna
A wani bayani da ya rattabawa hannu, shugaban babban banki kasar Najeriya, ya bukaci gwamnatin Muhammadu Buhari ta yiwa mutane cikakken bayani kan kama Nnamdi Kanu da neman kama Sunday Iboho. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa.
“Ina kira ga gwamnatin Najeriya kan kama Nnamdi Kanu da tayi, hakan bai dace ba, kuma su tabbatar da sun Kare hakkin Nnamdi Kanu.”
“Haka kuma nayi bakin ciki, kuma bana goyon bayan harin da jami’ai suka kai gidan Sunday Iboho, wannan na nuna gwamnatin Najeriya na neman kulle bakin kowane dan kasa.”
“Don haka ina kira ga gwamnatin Muhammadu Buhari da jama’ar sa, kamar yadda sukai anfani da karfi wajan kama Nnamdi Kanu da neman kama Sunday Iboho, suyi amfani da wannan karfin wajan yima mutane cikakken bayani kan dalilin kama su.”
“Wannan shi zai bada damar hadin kai da zaman lafiya a Najeriya, sannan da duba ta’addanci dake faruwa a jahohin Arewa shima na daga cikin yankin Kasarmu.”
Comments 1