By Abbas Yakubu Yaura
A safiyar Lahadi ne aka sake gano gawar mutum guda daga cikin ginin bene mai hawa uku da ya ruguje a unguwar Yaba da ke Legas, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa hudu.
Ko-odinetan shiyyar Kudu-maso-Yamma,na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, Mista Ibrahim Farinloye, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya wannan ci gaba a ranar Lahadi.
Farinloye ya ce a cikin mutane biyun da suka tsira daga ginin da ya ruguje, daya ne kawai daga cikinsu ya makale yayin da mutum na biyu matashin ya tsira da sa’a bayan ya koka da jin yunwa.
Ya ce ginin ya ruguje ne ‘yan mintoci kadan bayan matashin ya bar gurin da ginin yake domin ya je sayo abinci.
Ko-odinetan shiyyar NEMA ya kara da cewa mazauna yankin sun hada kayan aiki domin ceton wanda ya tsira daga baraguzan ginin.
Farinloye ya ce an kammala aikin.
Sannan ya ce hukumar ta NEMA, hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas, hukumar kashe gobara, da kuma ‘yan sanda sun gudanar da aikin ceto tare da dawo da su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wani bene mai hawa uku a ranar Asabar ya ruguje a lamba 16, Akanbi Crescent, kusa da titin Adesina, Harvey, Sabo, unguwar Yaba a Legas, inda mutane biyar suka fada cikin lamarin.