By Abbas Yakubu Yaura
Dan takarar shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Bwari, Shekwogaza John Gabaya, ya yi nasarar lashe zaben karamar hukumar da aka gudanar ranar Asabar a babban birnin tarayya (FCT).
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a ranar Lahadi ta bayyana Gabaya na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban karamar hukumar Bwari.
Jami’in tattara sakamakon zaben karamar hukumar Bwari, Farfesa Amuche Madu, ya ce Gabaya wanda shi ne shugaban majalisar, ya samu kuri’u 13, 045 tare da bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Madu ya ce: “Shekwogaza Gabaya na PDP, bayan ya tabbatar da bukatun doka kuma ya samu kuri’u mafi yawa, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma aka dawo da shi.”
Ta kuma ce dan takarar jam’iyyar APC, Mista Haruna Shekwolo, ya samu kuri’u 7,697, yayin da na jam’iyyar APGA Abubakar Abdullahi ya samu kuri’u 603 inda ya zo na uku.
An gudanar da zaben shugabannin karamar hukumar Bwari a unguwanni 10 na majalisar da suka hada da Igu, Kubwa, Duste, Kawu, Byazin, Shere, Bwari Central, Kuduru da Usuma.
A ranar Asabar din da ta gabata ne aka gudanar da zaben karamar hukumar FCT a mazabu 68 da ke fadin Bwari, Abaji, Gwagwalada, Kuje, Kwali da Abuja Municipal Council (AMAC).
‘Yan takara 473 ne da jam’iyyun siyasa 14 suka dauki nauyin gudanar da zaben.
Mu bamuda wani dantara 2023 samada Alh Atiku Abubakar insha Allah, Domin shine zabunmu,Kuma Allah yabashi Ikon tafiyar da mulkinsa cikin Adalci fa jinkan talakawa,daga bakin sarkin Yakin Baba Atiku 4 president 2023, da iznin Allah.