Babban Shehin Darikar Kiristanci Fasto Enoch Adeboye ya ce zuciyar Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir el-Rufa’i zuciya ce ta alkhairi.
Fasto Adeboye wanda ke wannan ikirari a yayin da ya kai ziyara wa gwamnan a yau talata, ya ce a har kullum yana ci gaba da yi wa gwamnan da jihar Kaduna da ma kasa baki daya addu’o’i din cimma nasara.
Adeboye ya kara da cewa duk wani da ka ga yana sukar Alkiblar el-Rufa’i to lallai ba fahimci wanene shi ba shi ya sa yake haka.
“Mun san cewa kana da kalubale da Allah ne kaɗai zai maganace maka su, kalubalen sun karfin yadda mutane ke zato”
“Mun san juna da ni da kai tun ba yau ba,Na san kai Wanene, Na yadda kake ji, musamman kan matsalar sace sacen jama’a, na san yadda ka ji lokacin da aka fara sace ɗaliban Makaranta”
A maida jawabin shina Gwamna Nasir el-Rufa’i ya jajanta wa mambobin Chocin RCCG bisa garkuwa da fastocin su da aka yi a baya.
Ya ce gwamnatin sa na ci gaba da iya kokarinta na ganin ta ingan harkar tsaro a jihar