Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar wa alhazan Najeriya cewa za a ciyar da su abinci na gida yayin gudanar da aikin hajji a kasar Saudiyya. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da yake jawabi yayin kaddamar da jigilar maniyyatan Najeriya a ranar Alhamis, Shugaban Hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan ya ce, mahajjata ka iya samun amincin da suke so a yayin aikin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bankuna Yanzu Zasu Iya Bayar Da Katin Ƙasa – FG
Idan dai za a iya tunawa, an samu cece-ku-ce kan irin abincin da ake baiwa alhazan Najeriya a lokacin aikin hajjin 2022, wanda hakan ya sa hukumar ta maido da wa Alhazan kudaden da suka kai N107.8m (SR542,033) kan matsalar.
Amma a wannan karon Hassan ya ce sabon tsarin ka iya samar wa ‘yan Najeriya ayyukan yi a wannan lokacin.
Yayin da yake bayyana cewa an samu damar tattaunawa kan farashin da ya dace na masaukin ko otal din da za a bai wa Maninyatan Najeriya a Makkah.
Duk da kalubalen da rufe sararin samaniyar Sudan ya haifar, ya ba da godiya ga “Mai-duka don warware matsalar cikin ruwan sanyi.”
Hassan ya kuma bukaci maniyyatan da su kasance wakilan Najeriya nagari ta hanyar bin ka’idoji da dokokin Saudiyya.
A nasa jawabin, shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda karamin ministan kula da harkokin kasashen waje, Ambasada Zubairu Dada ya wakilta, ya yabawa hukumar NAHCON bisa nasarar kammala gudanar da shirye-shiryen aikin Hajjin 2023.
A wani labarin kuma, Gabanin Rantsarwa, Tinubu Yayi wa Yan Najeriya Wani Mahimmin Alkawari
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya sha alwashin ba zai ba ‘yan Najeriya kunya ba. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana haka ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama shi da lambar girmamawa ta kasa (GCFR) a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis.