Akwai katin zabe sama da dubu sittin da ba’a karba a Gombe, cewar INEC
Hukumar zabe ta Kasa ta koka kan irin nuna ko in kula da Mutanen jihar Gombe keyi kan karbar katin zaben su.
Hukumar ta ce “Sama da katin zabe dubu sittin ne wanda ba’a karba ba a jihar”.
KARANTA:-Gwamna Ganduje ya halarci Taron Masarautar jihar Kano
Alhaji Umar Ibrahim shugaban Hukumar ta zabe na Jahar Gombe, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Alhamis.
Ya kuma ce ” hukumar ta shirya tsaf don cigaba da yin rijistar katin zaben ga wadanda suka cancanta a Jahar.”
Ya cigaba da cewa ” za’a dauki tsawon shekara ana aikin yin rijistar, amma bai ga dalilin da zai sa Mutane suce sai lokaci ya kure sannan za suyi.”
Yace aikin kamata yayi a farashi tun a shekarar 2020, amman saboda cutar Covid-19 ta kawo cikas.
Yace “yin rijistar yanzu zai baiwa dama ga wadanda suka cika shekaru sha takwas, da wadanda suke son sauya mazabar su da kuma wadanda katin zaben nasu ya bata.”