Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya umarci ma’aikatar muhalli da ta hada hannu da ma’aikatu da ma’aikatar karamar hukumar Kontagora domin ruguza duk wasu gine-gine.
Gwamna ya ce hakan zata faru ne akan duk wani gini da ya hau kan hanyoyin ruwa.
Bello ya bada umarnin ne a ziyarar jajantawa mutanen da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a Kontagora.
Daga nan sai Gwamnan ya jajantawa Sarkin da wadanda suka rasa ‘yan uwansu, da kuma dukiyoyinsu a wannan bala’in.
KARANTA ANAN: Cutar Gudawa Na Hallaka Yara Dubu 124 A Najeriya – Sadiya Farouq
A nasa bangaren, Kwamishinan Muhalli na Jihar, Daniel Habila Galadima a nasa jawabin ya bada tabbacin cewa za a shirya tsarin da ake bukata na samar da mafita mai ɗorewa a cikin watan Satumban 2022, inda ya ƙara da cewa za a ƙara wayar da kan jama’a don gujewa gini akan hanyoyin ruwa.
Da yake jawabi, Sarkin Kontagora, Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu II ya gode wa Gwamnan bisa ziyarar da ya kai wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, inda ya ba shi tabbacin raba kayayyakin tallafi da ya bayar.
Haka kuma, shugaban karamar hukumar Kontagora, Alhaji Shehu Pawa ya tabbatar da cewa mutane 237 ne ambaliyar ruwan ta shafa sannan an samu mutuwar mutane biyu.
Gwamna Bello ya kuma ziyarci Hayin Hakimi, daya daga cikin al’ummomi shida da bala’in ambaliyar ruwa ta shafa, domin tantancewa a nan take.
A wani labarin kuma: Akwai Yiwuwar APC Ta Shiryawa Tinubu Wani Tuggu a 2023 – Takunbo Awolowo
Tokunbo Awolowo-Dosunmu, diyar dan rajin kishin kasa a Najeriya, Obafemi Awolowo, ta zargi yiwuwar juyawa Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.
Ta yi zargin cewa akwai wani shiri na kawar da Tinubu a nada abokin takararsa, Kashim Shettima a matsayin shugaban kasa.