Labaran da suke fitowa daga shafin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham dake ƙasar Ingila ya nuna cewar akwai yiwwuwar ta sayi ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United kuma ɗan asalin ƙasar Ingila wato Jesse Lingard.
Tottenham dai tun a ranar da ta fara fafata wasan farko na sabuwar kakar gasar ajin Firimiya ta bana wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 aka gigita ta a har gida daci 1 mai ban haushi wato cin da Everton ta yimata.
Hakan ya sanyasu neman ‘yan wasa domin yin gyara da kyakykyawan garambawul a ƙungiyar ta yadda zasu kai gaci a kakar wasa ta bana tunda kusan kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa a ƙasar ta Ingila tayi cefane domin tunkarar kakar wasa ta bana.
Tottenham dai ta bayyana cewar zata biya Manchester United £30m domin ta bata Jesse Lingard, idan za a iya tunawa Tottenham ta sayi ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid guda biyu a tsakiyar makonnan wato Sergio Reguilon da Gareth Bale sai dai Bale a matsayin aro yake na shekara guda.
A wannan rana ta Lahadi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham tasami nasara a wasan mako na biyu inda ta ragargaza Southampton daci 5 da 2 inda a yanzu take da maki 3 daga cikin wasanni guda 2 data fafata.