By Abbas Yakubu Yaura
Wani matashin dan soyayya mai suna Muyiwa ya hadu da babbar masoyiyarsa Thereza a lokacin da yake neman gidan haya yayin da ya ci gaba da karatunsa na jami’a.
Tsohuwar wacce ke da ‘ya’ya 8 da jikoki 20 ita ce mai gidan da Muyiwa da abokinsa suke zaune.
DUBA WANNAN LABARIN: An Kama Wani ASP A Legas Bisa Karbar Cin Hancin Naira 50,000 Daga Hannun Wani Mai Yiwa Kasa Hidima
Duk da tazarar shekaru 60 a tsakaninsu, wani matashi dan shekara 25 mai suna Muyiwa yana soyayya da wata tsohuwa mai shekaru 85 mai suna Thereza.
Shi da abokan aikinsa sun sami kansu a gidan Thereza a kasar Kenya inda suke yin zaman haya suka koma ciki.
Muyiwa ya shaidawa Afrimax cewa ya bar kasarsa Kongo zuwa wata kasa ta Afirka da (ba a bayyana ba) da nufin ci gaba da karatunsa na jami’a.
Yana cikin zama a wurin, wani lamari ya sa ya gane ita ce gare shi.
Muyiwa ya ce sauran matan daya ke so a baya sun kasance masu ban mamaki, amma Thereza ta bambanta kuma tana fatan ba za ta rigashi mutuwa ba.
Akan yadda suke soyayya, Muyiwa ya tuno wani lamari da ya faru a wata juma’a mai kaddara.
“Na tuna wata Juma’a da abokin aikina ba ya nan, yunwa nake ji kuma ba mu da abinci, na yi rauni sosai, kuma daga nan ba inda naje sai tsohuwar nan ta kawo mini abinci, ta zo ta yi mini hidima da kulawa sosai.” “ya tuna.
A cewarsa, wannan na daya daga cikin halaye da dama na macen da ya samu ta same shi.
Ya kara da cewa “Yadda ta yi da ni ne yasa na so ta. Ko da yake ita tsohuwa ce kuma a gaskiya tana iya zama kakata, to me! Ina son ta,” in ji shi.
Shawarar yabo ga kanwarta, mahaifiyar yara 8 da jikoki 20 ta ce tana son Muyiwa kamar yadda yake sonta.
Thereza ta ce a shirye ta ke ta yi kasadar hakan duka saboda alakar su.
Ta ce: “Ni ‘yar shekara 85 ce, ina da ‘ya’ya 8 da jikoki 20, a cewar shekarun saurayina, zai iya zama jikana na 5, yana so na, ni ma ina son shi, yanzu na shirya tsaf don saka bikin auren mu riga da kuma zobe na cin amarci.”
Comments 2