Modu Bukar, Daraktan hukumar fasaha da al’adu na jihar Yobe ya shawarci ‘yan Nijeriya da su rika amfani da goruba saboda yadda take da amfani ga lafiyar dan Adam.
Bukar ya bada wannan shawarar ne a ranar Asabar a yayin ganawarsa da manema labarai a rumfar al’ummar Yobe a yayin taro kan kayayyakin al’adu na duniya a Abuja.
Modu Bukar, ya ce busasshiyar Goruba tana maganin cututtuka daban-daban da suka hada da; ciwon suga, borin jini, murdewar ciki, zafin ciwon da ake ji a lokacin hatsura.
Sannan ya kara da cewa; “Allah ya albarkaci mutanen jihar Yobe da Goruba. Kuma muna tanadinsa ta hanyar busar da shi.” In ji shi.
Ya ci gaba da cewa; ga macen da take jin zafi bayan ta haihu, ana sanya goruba cikin ruwa na dan wani lokaci, sannan a bata ta sha. Sannan ya tabbatar da cewa kowanne mutum zai iya amfani da Goruba a lokacin da ya samu murdewar ciki. Kuma ya ce za a iya cin Goruba kamar yadda ake cin goro.
“Sai dai ba a ko’ina ake samun Goruba a fadin kasarnan.” In ji shi.
Bukar ya ce har wala yau suna amfani da ganyayyaki a matsayin raffia wajen sakar tabarma. Ya kara da cewa; Nijeriya Allah ya yi mata albarka da maganguna daban-daban da itatuwa masu albarka, wanda ya ce wanda al’ummar duniya za su yi amfani da su wanda hakan ka iya bunkasa tattalin arzikin Nijeriya da kawo wa ci gaba. Bukar har wala yau ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da damar da suka samu wajen amfani da busasshiyar Goruba wanda za su iya samu da yawan gaske a jihar Yobe saboda wadatarsa a jihar.
Ya kuma tabbatar da cewa cin goruba ko shan sa a cikin ruwa ba shi da illa.
Buda baki da dabino kamin shan duk wani abin sha ko cin duk wani abinci,na kara lafiya da kuzarin mutum da kamar kaso sabain cikin dari.Sannan sunna ce ta manzon tsira(saw)fara buda baki da dabino.