Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya kaddamar da rabon litattafai 11,000 kyauta ga daukacin daliban manyan makarantun Sakandare (SSS 2) a makarantun gwamnati dake fadin jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ya ruwaito cewa, litattafan sun hada Chemistry da Physics kyauta, wanda Alh Ahmed Ododo, Babban Odita na Kananan Hukumomin Kogi, wanda ta dauki nauyi kuma ya bada tallafin don tallafawa shirin tallafin karatu da jagoranci na Gwamnatin Jihar.
Da yake jawabi a wajen bude taron a Kwalejin tunawa da Abdulaziz Atta da ke Okene, Gwamnan ya yabawa masu ba da gudummawar wajen tallafawa harkokin ilimi a jihar.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Bello, wanda Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar, Mista Wemi Jones ya wakilta, ya ce Gwamnatinsa ta bai wa ilimi fifiko, musamman Kimiyya, Fasaha, Injiniyanci da Lissafi (STEM).
KU KARANTA KUMA Kwalejin Fasaha A Jihar Kogi Ta Sake Korar Wasu Daliban
Gwamnan ya jaddada cewa, kudirinsa na inganta fannin ilimi a jihar, ya sa aka ware kashi 30 cikin 100 na ilimi a cikin kasafin kudin shekarar 2022, har ma ya wuce ma’auni na UNESCO na kashi 26 cikin 100.
Ya ce hakan ya nuna yadda ake gudanar da manya-manyan ayyukan samar da ilimi, da kuma daukar kwararrun malaman makarantun sakandare a fadin jihar.
Bello ya ce baya ga gina gine-ginen makarantu, gwamnati ta kuma himmatu wajen samar wa makarantun da kwararrun malamai.
Ya bayyana cewa daukar malamai ma, ya kai matakin karshe ne bayan an kammala gwaje-gwajen sanin makamar aiki da kuma tattaunawa ta baka, yana mai cewa jerin sunaye na karshe yana nan yana na jiran amincewa ta karshe.
Gwamnan ya shawarci daliban da su tabbatar da kokarin masu ba da gudummawar ta hanyar yin amfani da litattafan karatu yadda ya kamata.
Majiyar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa manyan baki da iyayen sarautu da tsofaffin daliban makaranta da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi ne suka halarci bikin.
Shugaban karamar hukumar Okene, Mista Abdulrasak Mohammad; Ohi na Adavi, HRH Alh. Muhammad Bello, ya yabawa mai bayar da tallafin bisa wannan karamcin da kuma jihar kan wannan shiri. (NAN)
A Wani Labarin Kuma 2023: Tsagin PDP G5 Sun Zo Da Sabbin Bukatu Kafin Yi Wa Atiku Aiki
Da alamu dai rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya zo karshe bayan da shugabannin jam’iyyar suka cimma matsaya da gwamnonin PDP tsagin G5.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mambobin Gwamnonin PDP G5, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, sun yi takun-saka da Atiku, bayan da Wike ya kasa lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.