Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno, SEMA, ta ce akalla mutane 18,406 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kananan hukumomi 14 na jihar.
Darakta Janar na Hukumar Yabawa Kolo ce ta bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Maiduguri ranar Litinin.
Ta ce mutanen da abin ya shafa da suka hada da mata da kananan yara sun kauracewa gidajensu sakamakon ruwan sama da aka samu a bana.
KARANTA ANAN: Gwamnatin Kano Ta Daura Damarar Kawo Ƙarshen Cutar Tarin Fuka A Jihar
Ta lissafa yankunan da abin ya shafa sun hada da Shani, Kwaya Kusar, Biu, Damboa, Askira Uba, Chibok, Kaga, Dikwa, Maiduguri, Monguno, Jere, Mobbar, Gwoza, Monguno da Kala Balge da dai sauransu.
Shugabar hukumar SEMA ta ce aikin tantance barnar da aka gudanar a kananan hukumomin Monguno da Kala Balve ya nuna cewa ambaliyar ruwa ta mamaye filayen noma, inda mutane 1,735 suka rasa matsugunansu, sun lalata matsugunai 681 da bandaki 112 a sansanonin GGSS, NRC da Gana Ali.
“Rahotanni daga abokan huldar kasa da kasa a wurare daban-daban sun nuna cewa gidaje 4,989 sun lalace, sannan 16,393 abin ya shafa.
Yabawa ta bayyana cewa, kwamitin kula da ambaliyar ruwa na jihar, karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Usman Kadafur, ya dukufa wajen taimakawa wadanda bala’in ya rutsa da su.
A wani labarin kuma: Yan ta’adda Sun Sace Matar Aure, Da Yar’ta A Jihar Neja
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wasu mata biyu da wani mutum a kusa da otal din Niger Motel da ke unguwar Jepap a garin Suleja na jihar Neja.
Yan bindigar sun yi garkuwa da mutane hudu ciki har da wata limamin coci a yankin tare da wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu da aka biya wa wadanda suka sace su a matsayin kudin fansa kafin su samu ‘yanci.
Wata majiya a unguwar ta shaidawa DAILY POST cewa masu garkuwan sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 1:00 na rana a ranar Asabar, inda aka yi garkuwa da wata matar aure da diyarta ‘yar shekara 18 a lokacin da suka shiga gidan.