Mutane 7 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Magama da Rafi na jihar Neja. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Babban Daraktan Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Ahmed Ibrahim Inga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya ce an kashe rayuka shida a Magama da 1 a Rafi.
Ya kuma ce mutane da dama sun rasa gidajensu, da filayen noma, gadoji da wasu hanyoyi a kananan hukumomin Lavun, Magama, Rafi, Kontagora, Gbako, Mashegu da Wushishi.
Inga ya yi gargadin cewa har yanzu ana ci gaba da tantance illar ambaliyar ruwan, sannan ya yi kira ga al’umma da su share magudanun ruwa tare da gyara muhallansu, domin kauce wa kamuwa zazzabin cizon sauro.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Bindiga Sun farmaki Wani Masallaci Tare Da Sace Masallata
Ya kuma yi gargadin a guji yin gini a magudanan ruwa da zubar da shara a magudanun ruwa, kamar yadda ya yi kira ga al’ummomin dake kusa da kogin da su takaita ayyukansu a gefen kogin a lokacin damina.
“Mafi dacewa, mutanen da ke zaune a yankunan kogi ya kamata su ƙaura zuwa wurare mafi aminci da ake da su,” in ji shi.
A AWANI LABARIN KUMA: Ganduje Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoninsa
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni guda goma sha daya, a dakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata.
Gwamna ganduje ya hori sabbin kwamishinonin da suyi aiki tukuru bisa kwarewa domin sauke nauyin da aka dora musu inda ya sanar da ma’aikatun da aka tura su kamar haka;