Sama da mutane 80 ne ambaliyar ruwa ta kashe a Sudan tun farkon damina a watan Yulin shekarar Nan da mike cikin.
Mai magana da yawun majalisar tsaron al’umar kasar Sudan ya ce ”Mutane 84 ne suka mutu har lahira, yayin da 67 suka jikkata sanadiyar ambaliyar Ruwa a kasar.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya shafi akalla larduna 14 daga cikin 18 dake kasar, tare da lalata gidaje sama da 30,000. Ya kuma shafi amfanin gona da kayayyakin more rayuwa na jama’ar kasar ta Sudan.
Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa, akalla mutane 102,000 ne ruwan sama mai karfi, da ambaliyar ruwa ya shafa a fadin kasar
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani mutum ya kashe Direban Keke Napep da duka a Kwara
A bara, Sudan ta ayyana dokar ta -baci ta kasa, na tsawon watanni uku, saboda ambaliyar ruwa da ta kashe mutane kusan 100, kana ta shafi mutane sama da 600,000, tare da lalata gidaje sama da 100,000 a kasar.
A wani labarin Kuma na daban
Kwamitin Ruko na Jami’iyyar APC na Kasa, a ranar Talata ta nada Kwamitin sasanci na Jami’iyyar na Kasa.
Mambobin Kwamitin sun hada da; tsohon Gwamnan Jahar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu, da Ministan Ayyuka na Musamman George Akume, da tsohon Gwamnan Jahar Enugu Sullivan Chime, da sauran su.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Jami’iyyar na Kasa John Akpanudoedehe ya fitar a Abuja, inda yace Jami’iyyar ta nada Adamu, da Akume, da Dogara, da Chime, da Adebule, da sauran su a matsayin Kwamitin sasanci na Jami’iyyar na Kasa.
Sanarwar tace ” Shugaban Kwamitin Ruko na Jami’iyyar na Kasa Mai Mala Buni ya amince da nada Kwamitin sasanci na Kasa da suka hada da;
“Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaba, da Otunba Moses Alake Adeyemo a matsayin Sakataren Kwamitin, da Sanata George Akume, da Sullivan Chime, da Ali Saad Birnin Kudu, da Yakubu Dogara, da Alhaji Suleiman Argungu, da Mrs Olurati I. Adebule da Dr. Mrs. Beta Edu.
Haka Zalika, za’a sanar da ranar kaddamar da mambobin Kwamitin Sasancin.