An zargi wani Mutum da dokan wani Mai a dai-dai-ta Sahu Wanda yayi sanadiyar mutuwar shi har lahira a garin Ilorin babban birnin jihar Kwara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Wanda ake zargin da wannan aika-aika Mai suna Kayode Oluwatomi Wanda akafi Sani da “Lawyer”, ma’aikaci ne a Kamfanin Tuntubar na BYC dake yankin Irewolede a garin Ilorin.
An kuma bayyana cewa, ya daki Mamacin ne Mai suna, Kayode Oluwatomi wanda yayi sanadiyar mutuwar sa, sakamakon ya daki motar shi ta baya.
A cewar wani shaidan gani da Ido, lamarin ya afku ne, bayan mutanen biyu sun fara muyan yawu a tsakanin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar APC ta nada Kwamitin Sasanci
Kazalika shaidan ya ce, “Mutumin da ake zargin ya bugi mai keken Napep din ne da wani abu da ake kyautata zaton cewa laya ne, sai mutumin ya fadi ya mutu nan take.” Inji shi
“An ajiye gawarsa Asibitin Garin Alimi, dake yankin Asa Dam, inda kuma daga bisani yan sanda suka ci gaba da binciken lamarin ,” inji shaidar.
Kazalika Koda majiyar jaridar Dimokuradiyya ta tuntumi jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kwara Ajayi Okasanmi, ya tabbatar wa da manema labarai afkuwar lamarin
Inda ya ce, rundunar ta Sami rahoton afkuwar lamarin ne ta bakin Mataimakin Shugaban kungiyar masu Adai-daita Sahu dake yankin Asa-Dam na garin Ilorin.
A karshe ya ce, tuni jami’an rundunar Yan sanda ta cika hannu da Wanda ake zargi, Kuma za ta gurfanar da shi a gaban Kotu da zarar ta kammala gudanar da bincike.
A wani labarin Kuma na daban.
Akalla Mutane 10 ne suka rasa rayukan su, sakamakon hadarin mota a kan hanyar Gabasawa dake jihar Kano.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya faruwar lamarin.
Inda ya ce, lamarin ya faru ne jiya litinin a kan hanyar Gabasawa zuwa cikin garin Kano, bayan da direban mota Kiran Volkswagen Golf 3, ya rasu shanyo kan motar.
Kazalika Haruna Kiyawa ya ce, sakamakon hakan, fasinjoji goma sun mutu, yayin da wasu suka samu mummunan raunuka.
Comments 1