Akalla al’ummomi goma sha daya suka bar yankunan su sakamakon ambaliyar ruwa a karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Shugaban karamar hukumar Shehu Sule Udi ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Ringim.
Ya ce al’ummomin sun bar muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa da aka saba yi a kowace shekara, wanda kuma ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, da lalata daruruwan gidaje da filayen gonaki da sauran dukiyoyi sakamakon cikar dam din Tiga da ke jihar Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Peter Obi Ɗan Takarar Shiyya ne – Reno Omokri
Ya bayyana cewa ambaliyar ta kori al’ummar Dabi, Majiyawa, Dingare, Gabarin, Yandutse, Malamawar Yandutse, Cori, Gujaba, Sankara, Auramo da Garin Gada.
Udi ya ce karamar hukumar ta kwashe wadanda abin ya shafa tare da mayar da su sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Ringim da Gerawa tare da ba su abinci da ruwan sha da magunguna.
Shugaban karamar hukumar, ya bukaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da sauran daidaikun jama’a da su kawo dauki cikin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.
Malam Ibrahim daya daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa a kauyen Majiyawa, ya ce ambaliyar ta tafi da gidajensu da dukiyoyinsu da suka hada da abinci da tufafi.
Daily Trust ta ruwaito cewa akalla mutane takwas ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da biyar suka samu raunuka sakamakon wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar mako guda da ya gabata.
A WANI LABARIN KUMA: Zabtarewar Bango ta Danne wani mutum a Jigawa
Wani matashi mai shekara 28 mai suna Umar Sale ya mutu sakamakon faɗowar bango a karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa.
Kakakin hukumar NSCDC, CSC Adamu Shehu, ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin.