A ƙalla gidaje sama da 300 ne Ambaliyar ruwa ta shafe su a birnin Jalingo fadar gwamnatin jihar Taraba.
Wasu mazauna yankin sun shaida cwwa Ambaliyar ruwan ta fara ne tun da sanyin safiyar ranar Asabar sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi.
Ko da yake kuma al’ummar sun garuruwan da al’amarin ya shafa kazalika sun ce akwai yiwuwar ambaliyar na da alaka da sakin ruwa daga wani dam da kasar Kamaru ta yi.
Duk da yake babu asarar rai sakamakon ambaliyar ruwan, to sai sai hakan ya yi sanadiyar tsayuwar lamura chak a birnin.
Kuma tuni jami’an hukumar bada agaji ta Red Cross suka isa inda lamarin ya wakana don bada agajin gaggawa.
Wasu mazauna garin da ibtila’in ambaliyar ruwan ya shafa sun bukaci gwamnati da ta gaggauta basu agaji ta hanyar samar musu da matsugunai.
Comments 1