Ambaliyar ruwa ta ruguza Al’ummomi 225 a Kano da Jigawa — NEMA
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta ce ambaliyar ruwa ta shafi al’ummomi 225 biyo bayan mamakon ruwan sama da aka dade ana yi a kananan hukumomi 31 na jihohin Kano da Jigawa daga watan Yuli zuwa yau.
Dokta Nuradeen Abdullahi, Jami’in Hukumar NEMA a ofishin yankin Kano/Jigawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nan ba da jimawa ba za mu fallasa sunayen Manyan Mutane masu Satar Mai – Garba Shehu
Ya ce hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) a ranar 16 ga watan Agusta ta yi hasashen za a samu ruwan sama ba kamar yadda aka saba a jihohi 19 tsakanin watan Agusta da Satumba da suka hada da Kano/Jigawa, ya kuma yi kira ga jihohin da abin ya shafa da su kara kaimi wajen shara da kuma daukar matakai.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Tudun Wada; Doguwa, Kibiya, Kiru, Gwale, Danbatta, Bagwai, Ajingi, Albasu, Shanono, Tsanyawa, Rimin Gado da Dawakin Kudu a jihar Kano.
Yayin da yake Jigawa, bala’in ya shafi Kafin hausa; Malam madori, Hadejia, Guri, Auyo, Birniwa, Jahun, Miga, Kiyawa, Birnin Kudu, Kaugama, Babura, Gwaram, Dutse da Kirikasamma
Abdullahi ya ce ambaliyar ta lalata gidaje da dama da kayayyakin more rayuwa da filayen noma da dabbobi da dukiyoyi tare da raba daruruwan mutane daga gidajen su.
“Ina roƙon hukumomi da masu ruwa da tsaki da su ƙaura daga wurin dake da hatsari zuwa wajen da bai da hatsari, tare da fitar da ingantaccen tsarin shirye-shiryen gaggawa,” in ji shi.
Ya bukaci gwamnatocin jihohi su fara wayar da kan jama’a akan yiwuwar ɗaukar mataki musamman a wuraren da ke da hadari don dakile bala’i.
Jami’in hukumar ta NEMA ya kuma shawarci mazauna yankin da su rika bin sakonnin gargadin da wuri, share magudanun ruwa da sauran hanyoyin ruwa don wucewa cikin sauki.