Akalla
mutum 29 ne ambaliyar ya ci rayukansu a kasar Kenya kamar yadda hukumomin kasar
suka tabbatar a ranar Alhamis.
Sashen lura da yanayi na kasar Kenya, sun gargadi al’umma cewa akwai yiwuwar ruwan sama zai ci gaba da sauka a kasar.
Kasar dake gabashin Afrika na fuskantar ruwan a karo na biyu cikin shekara daya.
James Muhindi daga sashen lura da yanayi, ya shaidawa manema labarai cewa; ruwan saman a watan Oktoba ya zarce yadda ake tunani a dukkanin fadin Kenya.
Ya ce akwai wani yanki dake kusa da iyakar kasar da kasar Habasha da aka yi musu ruwan sama cikin kwanaki 10 a wata guda fiye da ko’ina.
Ya tabbatar da cewa; fiye da mutum dubu 12 suka bar muhallansu saboda ambaliyar ruwan.