Shugaba kasa Muhammadu Buhari da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a ranar Laraba a birnin Sochi dake kasar Rasha sun amince da bunkasa alakar dake tsakanin kasashen biyu domin ganin an kammala dukkanin ayyukan da aka bar su ba a kammala su ba wanda kasashen suka samar.
Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu, shi ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce shugabannin kasashen biyu sun kulla yajejeniyar a yayin taron da ake ci gaba da gudanarwa a kasar Rasha na kulla Alaka tsakanin Afrika da Rasha.
Kasashen biyu sun amince da gudanar da wadansu ayyukan da ya shafi cinikayya da kuma tsaro tare da zuba hannu jari, sannan har wala yau kasar Rasha za ta taimakawa Nijeriya a bangaren soji.
A cewar sanarwar, Nijeriya da kasar Rasha za su yi aiki tare wajen bunkasa bangaren man fetur na kasar.